6 Faburairu 2022 - 18:54
Al-kazeemi : ​Al’ummar Iraki Ba sa Bukatar Ganin sojojin Amurka A Kasarsu

A wata ziyara da Fira ministan kasar iraki Mustapha Al-kazeemi ya kai kasar Amurka a baya bayan nan ya gana da shugaban Amurka Joe Biden kuma sun tatttauna kan batun ficewar sojojin ta daga kasar iraki, a karshen wannan shekarar dama sauran wasu batutuwa na daban.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Wata majiyar labaran kasar iraki ta bayyana cewa har yanzu dakarun sojin Amurka za su ci gaba da zama a akasar Iraki a matsayin masu bada shawara , lamarin da ya jawo kunguyoyin gwagwarmaya a kasar da suka hada da kungiyar hizbullah suka nuna rashin amincewa da ci gaban da zaman sojojin Amurka a kasa a kowanne irin yanayi,

Jagoran kungiyar iraki national wisdom movement Ammar Hakim ya fadi cewa babban manufar Alummar kasar shi ne samar da wani tsari da amintattun mutane da zasu jagoranci kasar ba tare da tsoma bakin wasu daga waje ba.

Daga karshe ya nuna cewa kungiyarsu tana sahun gaba wajen kare hadin kai tsakanin bangarorin siyasar kasar, kuma muna son a samu irin wannan hadin kai da fahimtar juna a mataki na kasa.

342/